in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babu alamun an kulla wata yarjejeniyar kawo zaman lafiya tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu kafin ran 2 ga watan Augusta
2012-08-03 17:30:57 cri
Kafin ran 2 ga watan Agusta, wato karshen lokacin kulla yarjejeniyar kawo zaman lafiya tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu da kwamitin sulhu na M.D.D. ya tabbata cewa wakilan kasashen biyu sun sake soma sabon zagaye na tattaunawa kan batun kawo zaman lafiya tsakanin kasashen biyu a birnin Addis Ababa na kasar Habasha a kokarin daidaita rikice-rikicen dake tsakaninsu a fannonin man fetur da ikon mallakar wasu yankuna. Bayan da rikicin nuna karfin tuwo ya barke a kan iyakar dake tsakanin kasashen biyu a watan Afrilu na bana, an yi ta jinkirtar ko kuma dakatar da shawarwarin kawo zaman lafiya a tsakaninsu. Bisa kokarin da M.D.D., Tarayyar kasashen Afirka AU, da sauran bangarorin da abin ya shafa suka yi ne aka farfado da wannan shawarwari tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu. Yanzu gamayyar kasa da kasa sun sa ransu sosai kan sakamakon da za'a samu a wannan shawarwari. Bugu da kari, kasashen yammacin duniya, kamar Amurka su ma sun mai da hankalinsu kwarai kan yadda za a tabbatar da zaman lafiya tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu.

A makon da muke ciki, madam Hillary Clinton za ta kai ziyararta karo na farko a kasar Sudan ta kudu, inda za ta yi shawarwari tare da shuguba Salva Kiir Mayardit na kasar Sudan ta kudu. Dangane da haka kakakin majalisar gudanarwa ta kasar Amurka ta bayyana cewa, madam Hillary Clinton za ta jaddada goyon bayan da kasar Amurka ke nuna wa kasar Sudan ta kudu, kuma za ta sa kaimi ga kasar Sudan ta kudu da ta kulla wata yarjejeniyar kawo zaman lafiya tsakaninta da kasar Sudan kan batutuwan tsaro, man fetur da hakkin mazauna kasashen biyu.

A cikin wannan shekarar, M.D.D. ta fitar da wa'adin karshe, inda ta nemi kasashen biyu da dole su kulla wata yarjejeniya kan batun man fetur da ikon mallakar wasu yankuna baki daya kafin ran 2 ga watan Agusta. Idan ba za su iya cimma ma wannan bukata ba, za a rubanya takunkumi akan kasashen biyu gaba daya. Amma har yanzu ya kasance da akwai banbancin ra'ayoyi kan kusan dukkan batutuwan tsakaninsu. Sabo da haka, ana ganin cewa, babu alaman za'a kulla yarjejeniyar kawo zaman lafiya baki daya tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu a cikin lokacin da aka bukata.

Da farko dai, ya kasance da bambancin ra'ayi tsakaninsu kan maganar kan yaya za a daidaita batun raba ribar man fetur da kuma batun tabbatar da tsaro? Har yanzu ba su samu matsaya daya ba kan wannan magana ba. Bayan da kasar Sudan ta kudu ta samu 'yancin kai a ran 9 ga watan Yulin bara, huldar dake tsakaninta da kasar Sudan ya kara tsami. Ana ta samun rikicin fadace fadace tsakaninsu a kan iyakar kasashen biyu, har ma hakan na nuna yiyuwan irin wannan rikici zai zama wani yaki. Sakamakon haka, yanzu al'ummomin Sudan ta matsa wa gwamnatinsu lamba kwarai wajen tabbatar da tsaro. Don haka, tabbas ne, a idon gwamnatin Sudan, batun tsaro ya fi muhimmanci, kuma ta dauki kwararan matsayi kan batun tsaro. Amma a ganin gwamnatin kasar Sudan ta kudu batun tattalin arziki ya fi muhimmanci sabo da yawan kasafin kudin da take samu daga man fetur ya kai kashi 90 cikin kashi dari. A watan Mayu na bana, saurin raguwar darajar kudin kasar Sudan ta kudu ya karu zuwa kashi 80 cikin kashi dari. Don haka, a ganin gwamnatin Sudan ta kudu, daidaita batun man fetur ya fi kome muhimmanci.

Sannan, har yanzu kasashen biyu ba su iya cimma daidaito ba kan batun ikon mallakar yankin Abyei. Yanzu, kasashen biyu kowannensu na da sojoji da 'yan sanda a wannan yankin da girmansa ya kai murabba'in kilomita kimanin dubu 10. Kasar Sudan ta kudu tana fatan wata hukumar yanke hukunci ta kasa da kasa za ta iya taimakawa wajen daidaita wannan batu, har ma tana fatan kungiyar AU da M.D.D. za su iya tsara wani shirin jefa kuri'ar raba gardama kan matsayin yankin Abyei, inda al'ummomin yankin za su iya halarta. Amma kasar Sudan ba ta mayar da martani ba kan wannan shawarar kasar Sudan ta kudu.

Game da dalilin da kome ya sa kasashen Sudan da Sudan ta kudu suka kasa cimma yarjejeniyar kawo zaman lafiya tsakaninsu ba? Manazarta suna ganin cewa, rashin aminci tsakanin kasashen biyu shi ne ya zama babban dalilin da ya sa haka. A 'yan kwanakin nan, shugaba Omar al-Bashir ya ki amincewa da shawarar da kungiyar AU ta bayar ta yin shawarwari tare da takwaransa Salva Kiir Mayardit na kasar Sudan ta kudu a ran 31 ga watan Yuli a kasar Habasha. Game da wannan, Kasar Sudan ta yi bayani cewa, wannan lokaci ya zo daidai da lokacin yin ziyarar Shugaba El-Bashir zuwa kasar Qatar. A waje daya, kasar ta Sudan ta bayyana fatanta na cewa, shugabannin kasashen biyu za su gana da juna bayan da wakilansu suka cimma matsaya daya kan dukkan batutuwa. Haka kuma, kafin a fara wannan shawarwarin kawo zaman lafiya tsakanin kasashen Sudan da Sudan ta kudu, wani jami'in hukumar Sudan ta kudu ya gaya wa kafofin watsa labaru cewa, ko ba za a iya kulla wata yarjejeniyar kawo zaman lafiya baki daya ba, M.D.D. ba za ta dauki matakin sa takunkumi ga kasashen biyu cikin hanzari ba.

Ta yaya za a iya sa kaimi kan kasashen Sudan da Sudan ta kudu wajen ganin sun samu zaman lafiya tsakaninsu? ya zama wani kalubale mai babba da ya kasance a gaban gamayyar kasa da kasa, kuma ana bukatar a ci gaba da yin kokari. (Sanusi Chen)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China