in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugban kasar Sudan ya tabbatar da kafa dokar ta-baci a yankin iyakar kasar da Sudan ta Kudu
2012-04-29 20:57:37 cri
Ranar Lahadi 29 ga watan da muke ciki, Omar al-Bashir, shugaban kasar Sudan, ya tabbatar da kafa dokar ta-baci a wasu wuraren dake yankin iyakar kasarsa da kasar Sudan ta Kudu, kamar yadda wata kafar watsa labarai ta kasar Sudan (SMC) ta bayyana.

A ranar 10 ga watan Afrilu, sojojin kasar Sudan ta Kudu sun mamaye yankin Heglig, lamarin da ya tsananta halin kiki-kaka dake tsakanin bangarorin Khartoum da ma Juba.

Duk da haka, a kwanakin baya sojojin kasar Sudan sun samu damar sake mallakar Heglig, yankin da ya kunshi rijiyoyin mai mafi girma na kasar Sudan, bayan da suka yi kazamar musayar wuta tare da sojojin kasar Sudan ta Kudu.(Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China