in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
An kammala shawarwari a tsakanin Sudan da Sudan ta kudu
2013-01-07 16:34:15 cri
An kammala shawarwari na kwanaki biyu a tsakanin shugaban kasar Sudan Abdullah Bashir da shugaban kasar Sudan ta Kudu Salva Kiir Mayardit a ranar 5 ga wata da dare, inda bangarorin biyu suka cimma daidaito kan batun kafa yankin da babu kasancewar soja a iyakokin dake tsakaninsu, amma akwai sauran matsalolin da ba su warware ba.

An gudanar da shawarwari a tsakanin Sudan da Sudan ta kudu a birnin Addis Ababa dake kasar Habasha, an ce, abin da ya fi jawo hankalin kasa da kasa a gun shawarwarin shi ne amincewa da kafa wani yankin da babu kasancewar soja a iyakokin dake tsakanin kasashen biyu, wannan zai taimaka wajen dawo fitar da man fetur daga kasar Sudan ta Kudu zuwa kasashen waje. Kana kasar Sudan ta Kudu ta amince da yin alkawari a rubuce kan katse huldar dake tsakaninta da jam'iyyar 'yantar da jama'ar Sudan(SPLM) dake kasar Sudan. Wato kasar Sudan ta Kudu za ta dakatar da nuna goyon baya ga SPLM dake kasar Sudan, wanda ya kasance kamar dakaru masu adawa da gwamnatin Sudan. Wannan shi ne abin da ya kawo cikas ga kasashen biyu wajen cimma yarjeniyoyi daban daban a watannin da suka gabata. Hakazalika, kasashen biyu sun yi alkawari cewa, za su aiwatar da yarjeniyoyi 8 kan hadin gwiwarsu da suka cimma a watan Satumba na shekarar bara a dukkan fannoni, sannan za su tsara jadawali game da yadda za a aiwatar da wannan aiki.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, hukumomin kula da harkokin siyasa da tsaro na kasashen biyu za su sake yin shawarwari a ranar 13 ga wata a kasar Habasha don tabbatar da kafa yankin da babu kasancewar soja da kuma gudanar da ayyuka bisa yarjejeniyar kiyaye tsaron iyakokin kasa a tsakaninsu da aka tsara. Game da yarjejeniya kan iyakokin kasa a tsakanin kasashen biyu da aka kammala cimma kashi 80 cikin kashi dari, shugabannin kasashen biyu za su sake yin ganawa don amince da ita bayan da kwamitocin yin shawarwari na kasashen biyu suka tsara jadawali kan wannan aiki.

Bayan da aka kafa kasar Sudan ta Kudu a shekarar 2011, ana ta samun matsaloli da dama a tsakaninta da Sudan a fannonin samar da man fetur, yin jigila da kuma yadda za a raba kudin shigar man da dai sauransu, wannan ya sa ake samun rikice-rikice a kan iyakokin dake tsakaninsu. Ko da yake an samu ci gaba a wannan shawarwarin dake tsakanin shugabannin kasashen biyu, amma suna da sauran tafiya kafin a kawo karshen takaddamar dake tsakaninsu. Alal misali, ba a warware matsalar mallakar yankin Abyei mai albarkatun man fetur a gun shawarwarin ba, ana saran gabatar da matsalar a shawarwari na gaba. Kana bangarorin biyu ba su cimma daidaito kan matsalar samar da man fetur da yin jigilar shi ba.

A ganin manazarta, burin shawarwarin a wannan karo shi ne warware matsaloli dake tsakaninsu a fannin tattalin arziki, a maimakon warware rikice-rikice dake tsakaninsu. A sakamakon halin nuna kiyayya dake tsakanin Sudan da Sudan ta Kudu da ake ciki a yanzu, lamarin ya haifar da babbar illa ga bunkasuwar tattalin arziki da zamantakewar al'ummar kasashen biyu. Kasashen biyu dukkansu sun nuna kiyayya ga juna ne don kawar da hankalin da jama'arsu suka maida kan matsalar tattalin arziki da cin hanci. Amma tsohon shugaban kasar Afirka ta Kudu mai shiga-tsakani kan rikicin Thabo Mebeki ya ce, shugabannin kasashen biyu sun amince da hadin gwiwarsu da aiwatar da yarjejeniyar da suka cimma, kuma shawarwarin da suka yi a wannan karo sun aza harsashi ga shawarwari a tsakaninsu na nan gaba. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China