Falesdinu ta amince da yin shawarwari tare da Isra'ila
Ran 24 ga wata, babban sakataren kwamitin zartarwa na hukumar neman yancin kan Falesdinu Yasser Abed Rabbo ya gaya wa manema labaru na kamfanin Xinhua cewa, bayan kai komo na shiga tsakani da Amurka ta yi, hukumar Falesdinu ta riga ta amince da komawa teburi tare da kasar Isra'ila don sa kaimi ga maido da shawarwarin kai tsaye tsakanin bangarorin biyu. Ya kuma bayyana cewa, sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Forbes Kerry ne zai jagorantar shawarwarin na nan gaba na tsawon lokacin mako-mako guda takwas bisa la'akari da ajandar da aka tsara, kuma yayin shawarwarin, Kerry zai gana da wakilan bangarorin biyu daya bayan daya don karfafa fahimtar juna ta yadda za su iya maido da shawarwarin zaman lafiya na kai tsaye da ke tsakanin bangarorin biyu. (Maryam)
Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku