A wannan rana, bayan da Wu Sike ya gana da sakatare janar na fadar shugaban hukumar Falesdinu Tayeb Abdul Rahim, ya fada wa manema labaru cewa, makasudin zuwansa shi ne, don tattauna batun ziyarar shugaban Falesdinu Mahmoud Abbas zuwa kasar Sin. Bisa goron gayyata da gwamnatin Sin ta ba shi, shugaban hukumar Falesdinu Mahmud Abbas zai ziyarci kasar Sin a farkon watan Mayu, kuma zai zama shugaban dake yankunan Gabas ta tsakiya na farko da sabbin shugabannin kasar Sin za su gana, wannan ya nuna cewa, sabbin shugabannin kasar Sin sun dora muhimmanci sosai game da batun Falesdinu da Isra'ila, kana ya nuna matsayin da kasar Sin ta kan tsaya a kai na goyon baya Falesdinu.
Tayeb ya jinjinawa kasar Sin da ta nuna goyo ga shigar da Falesdinu a M.D.D., da taimakon da Sin ta samar don kafa hukumar gwamnatin Falesdinu. Ya kuma sake nanata anniya da bukatun hukumar Falesdinu wajen farfado da shawarwari tsakaninta da Isra'ila, wato dole ne Isra'ila ta amince da shirin kasashe biyu bisa iyakokin kasashen da aka shata a shekarar 1967, da daina gina matsugunan Yahudawa, da sakin Falesdinawa da aka tsare a kasar Isra'ila.(Bako)