A ranar 23 ga wata, Kerry ya gana da shugaban hukumar al'ummar Palesdinu Mahmoud Abbas a Amman, babban birnin kasar Jordan, inda daga bisani ya koma kasar Isra'ila. A wannan rana da dare, ya yi shawarwari tare da firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu, inda suka tattauna kan yadda za a sake bude shawarwarin shimfida zaman lafia a tsakanin Isra'ila da Palesdinu. Yanzu shekaru biyu ko fiye ke nan da aka dakatar da shawarwarin tsakanin Isra'ila da Palesdinu. Ba a cimma tudun fadawa a yayin da Obama yake kan kujerar shugaban kasar karo na farko ba. A yayin da shugaban kasar Amurka Obama yake ziyara a yankin Palesdinu da Isra'ila, ya yi alkawari cewa, Kerry zai yi kokarin taimakawa wajen warware matsaloli a tsakanin Palesdinu da Isra'ila, amma shugaba Obama bai gabatar da sabon shirin warware wannan batu ta hanyar diplomasiyya ba. (Zainab)