A wannan rana, yayin da Erekat ke zantawa da manema labaru, ya bayyana cewa, Falesdinu ta amince da ra'ayin da tawagar kasashen Larabawa ta gabatar bayan shawarwarin da aka yi tsakaninta da sakataren harkokin wajen kasar Amurka John Forbes Kerry a karshen watan da ya gabata a birnin Washington, wato, Falesdinu da Isra'ila za su amince da shirinsu a karkashin iyakokin kasashen biyu da aka shata a shekarar 1967 bisa tushen amince da musayar yankunan kasar kalilan. Haka kuma, Erekat ya yi nuni da cewa, wannan ba sabon ra'ayi ne ba, amma Falesdinu ta amince da shi. Yanzu, ana jiran martani daga bangaren kasar Isra'ila, idan ya amince da wannan shiri, to, Falesdinu da kasashen Larabawa za su ci gaba da shawarwari tsakaninsu.
A wata sabuwa kuma, bisa labarun da kafofin yada labaru na Isra'ila suka bayar, an ce, ofishin firaministan kasar Isra'ila ya ki amincewa da mayar da martanin game da matsayin da kasashen Larabawa suka tsayar a kai. Amma, ministan shari'a na kasar Isra'ila Tzipi Livni da ke kula da batun shawarwari da Falesdinu, ya yi maraba da wannan ra'ayi, kuma ya ce, wannan yana da muhimmanci sosai.(Bako)