in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Farfado da shawarwari tsakanin Isra'ila da Palestinu cikin lumana ya dace da manufar Isra'ila, in ji Netanyahu
2013-07-21 17:04:22 cri
A ranar Asabar 20 ga wata, firaministan kasar Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ba da sanarwar maraba da shelar da ministan harkokin wajen Amurka John Kerry ya yi, wadda ta kunshi cimma matsayar farfado da shawarwari tsakanin Isra'ila da Palestinu cikin lumana.

Netanyahu ya kuma ce, hakan ya dace da burin Isra'ila na cimma moriya bisa manyan tsare-tsare. A dai wannan rana Isra'ila ta bayyana cewa, za ta saki wasu fursunoni Palestinu da take tsare da su, a kokarin farfado da shawarwari tsakaninta da Palestinu.

Netanyahu ya furta cewa, farfado da shawarwarin a wannan lokaci ya dace da manufar Isra'ila, ya kuma yi godiya ga mista Kerry, kan kokarinsa na farfado da yunkurin tabbatar da zaman lafiya tsakanin Isra'ila da Palestinu, yana mai fatan bangarorin da batun ya shafa za su yi taka-tsantsan, yayin gudanar da shawarwarin. Bugu da kari Netanyahu ya kara da cewa, babban aikinsa shi ne kokarin kiyaye tsaron jama'ar Isra'ila, don haka zai ci gaba da tsayawa tsayin daka kan kudurin Isra'ila na samar da tsaro ga al'ummarta.

A wannan rana, ministan tsaron farin kaya, da tsare tsaren Isra'ila, Yuval Steinitz ya tabbatar da cewa, kasarsa za ta saki wasu Palatinawa da take tsare da su daki-daki, a kokarin farfado da shawarwarin dake tafe.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China