A cikin wata sanarwa da kakakinsa ya rabawa manema labarai, Ban ki-Moon ya bayyana matukar rashin jin dadinsa, game da rahotannin barkewar fadan kabilanci a kudancin Guinea, lamarin da ya yi sanadiyar asarar rayuka da dukiyoyi da dama.
Sanarwar ta kuma yi kiran da a kwantar da hankali, kana babban sakataren ya bukaci 'yan kasar ta Guinea, da su guji aikata duk wani abin da zai kawo rashin zaman lafiya tsakanin al'ummomin da ke kasar.
Bugu da kari ya jaddada muhimmancin samar da yanayin da ya dace na zaman lafiya da gudanar da zabukan 'yan majalisun da aka shirya gudanarwa a ranar 24 ga watan Satumban wannan shekara.
A cewar rahotanni, adadin wadanda suka mutu a fadan da ya barke a daren ranar Lahadi a yankin N'Zerekore da ke kudancin Guinea ya karu zuwa 54 kana wadanda suka jikkata ya doshi 100. (Ibrahim)