A ranar 27 ga wata, gwamnatin Guinea ta ba da labari cewa, wani rikicin da ya-ki-ci-yaki-cinyewa, tun daga ranar 21 ga wata a birnin Conakry hedkwatar kasar, ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 12, tare da jikkatar wasu kimanin 90.
A cikin wadanda suka rasu, mutane 7 sun rasu ne sakamakon harbin bindiga, kana kuma an yi amfani da wukake, da sanduna, da duwatsu wajen raunata wasu, hakan ya sa mutane 26 sun ji rauni masu tsanani, kuma ya zuwa yanzu, an yi musu aikin jinya a asibiti, an kuma bayyana cewa, akasarin mutanen da suka rasu matasa ne masu shekaru 15 zuwa 25.
Dalilin da ya sa aka samu rikici shi ne, sabo da zanga-zangar da jam'iyyar adawa ta yi, don nuna adawa da jam'iyyar dake kan mulki, kan batun tsara lokacin yin zaben majalisar dokoki bisa radin kanta. Rikicin da ya barke tun daga ranar 21 ga wata ya shafe mako guda. A wata unguwar da magoya bayan jam'iyyar adawa suke zaune, masu zanga-zanga matasa sun katse hanya, kuma sun gwabza fada mai tsanani da 'yan sanda da suka je don tabbatar da doka da oda.(Bako)