Majiyarmu ta ce, an tuhumi wani direba dan kabilar Konianke da yin sata a wani gidan mai na kasar, wanda hakan ya haifar da rikici, daga baya wani mai gadi na kabilar Guerze ya harbe shi, nan take kuma, ya rasa ransa. Wannan abu ya janyo daukar matakan ramuwar gayya daga kabilar Konianke, wanda hakan ya haifar da rikici tsakanin kabilun biyu, rikicin da ya yi sanadiyyar mutuwar mutane da dama, kuma aka kone gidajen jama'a da dama, tare da kwashe dukiyoyinsu. Ya zuwa yanzu, gwamnatin Guinea ba ta bayar da bayani kan asalin wadanda suka mutu ko jikkata ba.
Bayan aukuwar lamarin, rundunar 'yan sandan yankin ya fara daukar matakan daidaita shi ba tare da bata lokaci ba. Don kwantar da hankalin jama'a, yanzu, an kafa dokar hana fitar yawon dare, don hana sake aukuwar rikici. Ban da wannan kuma, gwamnatin Guinea ta yi alkawarin gudanar da bincike kan lamarin, a sa'i daya kuma ta bukaci bangarorin biyu da su kai zuciyar nesa, don tabbatar da hadin gwiwa tsakanin kabilu daban daban na kasar, da samar da zaman karko a yankin.(Bako)