Bugu da kari, shugaba Conde ya bukaci kwamitin zaben da dai sauran hukumomin da abin ya shafa da su dukufa wajen shirya ayyukan zabe.
A sa'i daya kuma, ya yi kira ga jam'iyyun daban daban da su shiga zaben cikin lumana don a tabbatar da yanayin tsaron zaben.
Ran 8 ga wata, kwamitin zabe mai zaman kansa na kasar Guinea ya kira taron dukkan mambobinsa, inda suka tsai da jadawalin zaben 'yan majalisar dokokin kasar, kuma an tsara wannan jadawali ne bisa yarjejeniyar da aka kulla a farkon watan da muke ciki, tsakanin jam'iyyar dake kan gadon mulki da jam'iyyar adawa, kan batun zaben 'yan majalisar dokoki, kuma ya kamata a gudanar da zaben bayan kwanaki 84 da kulla wannan yarjejeniya. Bisa tsarin mulkin kasar da aka tsayar an ce,
duk kudurorin da kwamitin zabe mai zaman kansa ya tsayar ba za su fara aiki ba sai bayan shugaban kasa ya amince da su. (Maryam)