Cewar shugaban majalisar dokokin kasar , Ibrahima Sory Diallo, ya sa hannu kan wannan yarjejeniya, kamar yadda shugabannin sojin da suka yi juyin mulki suka sa hannu wanda hafsan hafsoshin kasar Antonio Injai ya sama hannu a madadin su, da kuma jam'iyyun siyasa guda 25, wadanda suka hada jam'iyyar PRS ta Kumba Yala, wadda kafin juyin mulkin ta kasance babbar jam'iyyar adawa ta kasar. Jam'iyyar PAIGC ta tsohon firaminista Carlos Gomes Junior ba ta sa hannu ba kan wannan yarjejeniya.(Abdou Halilou).