in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Magatakardan MDD ya gamsu da ci gaba da aka samu dangane da tattauna kan zabe a Guinea
2013-06-12 16:45:28 cri

Magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya bayyana ranar Talata cewa, ya gamsu da ci gaba da ake samu kan tattaunawa tsakanin bangarori masu rigimar siyasa a kasar Guinea, inda sakamakon hakan aka cimma yin shimfidar gudanar da zabukan 'yan majalisa.

Cikin wata sanarwa da mai magana da yawun magatakardan MDD ya bayar, an ce magatakardan yana maraba da yadda bangarori a kasar Guinea ke yin shawarwari.

Magatakardan ya bukace su da su ci gaba da hakan domin a samu warwarewar sauran batutuwa da za su haifar da matakan gudanar da zabukan 'yan majalisa lami lafiya kuma ba tare da magudi ba.

Wakilin musammman na magatakardan MDD a Afirka ta yamma Said Djinnit ya kira taro ran 22 ga watan Mayu a Conakry, babban birnin kasar Guinea tsakanin fraministan kasar da shugabannin adawa.

Bayan an shafe makonni ana tabka rikici, jam'iyya dake mulki a kasar Guinea da jam'iyyun adawa sun cimma nasara yayin zaman tattaunawa ranar Lahadi inda ake ganin hakan zai kawo karshen kiki kaka na siyasa, a kuma samu gudanar da zabukan 'yan majalisa.

Ya kamata a gudanar da zaben 'yan majalisar watanni 6 bayan na shugaban kasa a cikin watan Nuwamba na shekarar 2010 domin a samu kawo karshen matsala da juyin mulkin soja na watan Disamba na shekarar 2008 ya haifar.

Shugaban kasar Guinea Alpha Conde a kwanan baya ya sanar da cewa, za'a yi zabukan 'yan majalisa ran 30 ga watan Yuni, inda hakan ya fusata masu adawa domin suna ganin cewa, gwamnati tana yin son ranta ba tare da tuntubarsu ba.

Zanga-zanga a kasar sakamakon zabe tsakanin masu mara bayan 'yan adawa, jami'an tsaro da magoya bayan shugaba Conde a birnin Conakry ya yi sanadin mutuwar jama'a da dama kana daruruwa sun samu rauni tun watan Maris. (Lami Ali)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China