in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wasu hare-hare sun hallaka kimanin mutane 31 a kudancin Iraki
2013-07-15 11:28:33 cri

Kimanin mutane 31 ne suka hallaka, baya ga wasu 92 da suka jikkata sakamakon wasu hare-haren kunar bakin wake da aka kaddamar a kudancin kasar Iraki ranar Lahadi 14 ga watan nan.

A arewacin Lardin Babil, wani dan kunar bakin wake ne ya tada bam da yake dauke a wani babban masallaci dake Mosayab, inda nan take mutane 12 suka hallaka, yayin da kuma wasu 25 suka ji raunuka.

Da take tabbatar da aukuwar hakan, wata kafar kamfanin dillancin labarai dake kasar mai suna NINA, tace wasu mutane 7 sun rasu, yayin da kuma wasu 5 suka samu raunuka, sakamakon wasu nakiyoyi da aka dasa jikin wasu ababen hawa a birnin Basra, mai nisan kilomita 550 daga kudancin birnin Bagadaza. Har ila yau wasu karin hare-hare sun auku a Karbala da Nasiriya, lamarin da ya haddasa karin asarar rayuka da dama.

Kawo yanzu dai babu wata kungiyar da ta dauki nauyin kaddamar da wadannan hare-hare, koda yake dai a baya reshen kungiyar Al-Qaida dake kasar ta Iraki, ya sha daukar alhakin irin wadannan hare-hare. Hare-haren kunar bakin wake dai na kara yawaita a kasar ta Iraki a halin yanzu, tamkar a shekarun 2006 da 2007, lokacin da kasar ta fada kazamin yanayin fadace-fadace tsakanin al'ummominta.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China