Jim kadan bayan abkuwar lamarin, ofishin kakakin babban sakataren MDD ya bayar da wata sanarwa, inda ya ce, babban sakataren MDD Ban Ki-moon ya yi Allah wadai da fashewar boma-boman a Baghdad, babban birnin kasar Iraki, tare da nuna jajantawa ga iyalan mutanen da suka mutu a sakamakon lamarin. Wakilin musamman na babban sakataren MDD mai kula da batun kasar Iraki Martin Kobler shi ma ya bayar da wata sanarwa a wannan rana, inda ya yi tir da wannan lamari, kana ya ce, babu wasu dalilan aikata wadannan hare-hare ba.
Ranar 20 ga watan Maris rana za ta cika shekaru 10 da barkewar yakin kasar Iraki. A kwanakin baya, an sha samun hare-hare da tashe-tashen hankali dake da nasaba da addini a kasar Iraki, lamarin dake kara ingiza kasar cikin rashin zaman lafiya. (Zainab)