Bisa labarin da wani jami'i mai kula da janye kayayyakin soja na ma'aikatar kula da sufuri na sojojin kasar Amurka ya bayar, an ce, tun lokacin da sojojin kasar Amurka da ke kasar Iraki suka kammala aikinsu na yake-yake soja a kasar a watan Agusta na shekarar bara zuwa yanzu, yawan kayayyakin sojojin kasar Amurka da aka janye daga kasar Iraki ya kai miliyan 1.7, kuma za a yi sufurin sauran kayayyaki kimanin miliyan 1 daga kasar Iraki a cikin watanni 5 masu zuwa.
Wannan jami'i ya kara da cewa, za a yi sufurin yawancin kayayyaki zuwa kasar Amurka, amma za a mika wa sojojin tsaron kasar Iraki da sojojin kasar Amurka da ke kasar Iraki da wasu kayayyakin soja. Saboda kasar Iraki ba ta yanke shawarar ko za ta yarda da jibge sojojin Amurka a kasar ko a'a ba, har yanzu ba a tabbatar da yawan kayayyakin soja da sojojin Amurka da ke kasar za ta janye daga kasar Iraki ba. (Abubakar)