in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mutane 186 sun rasu ko jikkata a sanadiyyar hare-hare a kasar Iraki
2013-07-03 15:12:59 cri

Bisa labarin da rundunar 'yan sandan kasar Iraki ta fidda ran 2 ga wata, an ce, a kalla mutane 35 sun rasa rayukansu, yayin da 151 suka jikkata a sanadiyyar hare-haren da suka faru a kasar a wannan rana.

Wani mutum daga rundunar 'yan sandan kasar Iraki wanda bai so a bayyana sunansa ba ya nuna cewa, a kalla an samu hare-haren boma-bomai dake cikin motoci sau takwas cikin wannan rana.

Ban da wannan, an kuma samu hari sau daya a garuruwan Samawah da kuma Amarah da ke kudancin birnin Baghdad, kana an samu hare-hare a hedkwatar lardin Diyala da ke gabashin kasar, Baquba, da kuma hedkwatar lardin Nineveh da ke arewacin kasar, a Mosul.

Ya zuwa yanzu, babu wanda ya sanar da daukar alhakin hare-haren na wannan rana.

Tun da aka shiga shekarar nan, an fuskanci aikace-aikacen 'yan ta'adda ko hare-hare a kasar Iraki a lokuta da dama, inda yanayin tsaro a fadin kasar yana tayar da hankalin jama'a. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China