Cikin sanarwar, Ban Ki-moon ya furta cewa, a gun taron an kammala shawarwari na zagaye da ya gabata lami lafiya, tare da share fage sosai domin tabbatar da daddale wata yarjejeniyar da ta shafi dukkan fannoni wadda kuma ke da matsayi na doka kafin shekarar 2015. Dadin dadawa, Ban Ki-moon ya yi kira ga gwamnatoci, da sassan cinikayya, da kungiyoyi da jama'ar kasa da kasa, da su gaggauta daukar matakai, a kokarin cimma burinsu na ganin karuwar zafin yanayin duniya zai zama kasa da 2℃ baki daya.
Bayan haka, Ban Ki-moon ya ce zai kara kokarin daukaka matsayin ma'aunin yanayi da tara kudi bisa yawan gurbatacciyar iskar da aka fitar da sauransu, da kokarta cimma burin rattaba hannu kan wata yarjejeniya tsakanin dukkan kasashen duniya a shekarar 2015 tare da shugabannin kasashen duniya. Bugu da kari, ya taya ma Qatar murnar cimma nasarar gudanar da wannan taro.
A daren ranar Asabar 8 ga wata, shugaban babban taron sauyawar yanayi na Doha, kana shugaban hukumar sa ido kan cin hanci da rashawa da gudanar da harkokin mulkin kasar Qatar, Abdullah bin Hamad al-Atiiyah ya yi shelar cewa, an zartas da jerin kudurori a gun babban taron Doha, ciki har da gyararren shirin takardar Kyoto.(Fatima)