Ban Ki-moon ya nuna rashin jin dadi kan kudurin Isra'ila na habaka matsugunan Yahudawa
Babban magatakardan Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki-moon ya ba da sanarwa ta bakin kakakinsa a ranar Lahadi 2 ga wata cewa, yana mai nuna damuwa da rashin jin dadi kan yadda kasar Isra'ila ta zartas da shirin kara gina wa Yahudawa 'yan share wuri zauna gidaje 3000 a gabar yamma ta kogin Jordan da gabashin birnin Kudus.
A sanarwarsa, Mista Ban ya ce, yadda Isra'ila ke gina matsugunan Yahudawa ya keta dokar kasa da kasa tare da karin cewa idan an samu damar gina wadannan matsugunan Yahudawa, batun zai gurguntar da kokarin da ake yi na neman sasanta rikicin dake tsakanin Isra'ila da Palasdinu. (Bello Wang)