Wata sanarwa da kakakin Mr. Ban ya bayar, ta ce, babban sakataren har ila ya yi Allah-wadai da munanan hare-haren da aka kai ranar Lahadi a garin Potistum, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ma'aikatan lafiya, ya kuma mika ta'aziyya ga iyalan wadanda lamarin ya rutsa da su.
Sanarwar ta ce, wadanda aka kashen suna aikin inganta rayuwar galibin jama'ar da ke cikin hadari ne, kuma irin wadannan hare-hare na iya takaita ayyukan ma'aikatan lafiya da al'umma ke matukar bukatar su, sannan zai yi tasiri ga kokarin da ake yi na inganta rayuwar jama'a a ko'ina.
Babban sakataren ya ce, ba za a amince da irin wadannan munanan hare-hare da ake kaiwa ma'aikatan lafiya a sassa daban-daban na duniya ba, don haka ya karfafawa dukkan kasashe gwiwar da su kare ma'aikatan lafiya, ta yadda za su ci gaba da aikinsu na inganta lafiyar al'umma da kare rayukansu. (Ibrahim)