Sanarwar ta ce, wadannan rikice-rikice sun haddasa mutuwar Palasdinawa da dama, kana fararen hula da sojoji daga bangarorin biyu wato Palesdinu da Isra'ila da dama sun ji rauni, don haka Ban Ki-moon ya maida hankali sosai kan lamarin.
Ban da wannan kuma, Ban Ki-moon ya sake yin kira ga dakarun Palesdinu dake zirin Gaza da su dakatar da kai hare-hare ga wurare daban daban na kasar Isra'ila ba tare da bata lokaci ba, kana ya yi Allah wadai da hare-haren da aka kai. Hakazalika Ban Ki-moon ya yi kira ga kasar Isra'ila da ta yi hakuri, da kuma yin kira ga bangarorin biyu da su yi kokarin magance tsanantar rikice-rikice a tsakaninsu tare da tabbatar da tsaron lafiyar fararen hula a kasashen biyu.
Bisa labarin da aka bayar, an ce, dakarun Palesdinu dake zirin Gaza da sojojin kasar Isra'ila sun kabsa a ranar 10 ga wata, lamarin da ya haddasa mutuwar Palesdinawa 5 kana mutane fiye da 40 suka ji rauni. (Zainab)