in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ban Ki-Moon ya yi Allah wadai da harin da aka kaiwa birnin Quetta na kasar Pakistan
2013-02-18 16:39:29 cri

A ran 17 ga wata, babban sakataren MDD Ban Ki-Moon ya ba da wata sanarwa ta bakin kakakinsa, inda ya yi Allah wadai da harin da aka kai birnin Quetta na kasar Pakistan, tare kuma da jaddada matsayin MDD na goyon bayan kasar Pakistan wajen yaki da ta'addanci.

Sanarwar da aka fitar ta bayyana cewa, Ban Ki-Moon ya yi tir da harin da aka kaiwa magoya bayan darikar Shi'a a ran 16 ga wata a birnin Quetta. Game da hakan, Ban –Ki-Moon ya nemi da a yanke wa wadanda suka yi ikirarin aiwatar da harin hukuncin da ya dace ba tare da bata lokaci ba.

A ranar 16 ga wata da yamma, an kai wani harin kunar bakin wake a wata kasuwa dake birnin, lamarin da ya yi sanadin mutuwar mutane 84, yayin da wasu 173 suka jikkata, ciki hadda mata da kananan yara.

Kafar yada labaru ta yankin ta ba da labari cewa, tuni wata kungiyar 'yan ta'adda da gwamnatin kasar ta tarwatsa ta sanar da daukar alhakin kai wannan hari. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China