A ranar Alhamis, magatakardan MDD Ban Ki-Moon ya yi maraba da sanarwar da kasashen Koriya ta Arewa da Koriya ta Kudu suka bayar kan amincewa da suka cimma na yin zaman tattaunawa.
Sanarwa da mai magana da yawun Mr. Ban ya bayar na mai bayyana cewa, magatakardan ya ce, wannan mataki ya dace a kokarin da ake na rage zaman dar-dar da kuma bunkasa zaman lafiya da dorewa a yankin Koriya.
A ranar Alhamis ne kasar Koriya ta Kudu ta bayyana cewa, za ta yi zaman tattaunawa tsakanin ministoci, da Koriya ta Arewa, bisa shawara da Koriya ta Arewan ta gabatar na yin tattaunawa dangane da sake bude shiyyar masana'antu ta hadin gwiwa.
Mr. Ban ya yi kira ga kasashen biyu da su yi amfani da wannan dama wajen kara bunkasa ci gaba da aka samu, tare da nuna fatan cewa, za ta zamo wani tushin gina aminci tsakaninsu, in ji sanarwar. (Lami)