in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka a shirye take da ta yi shawarwari da Koriya ta Arewa
2013-04-19 09:47:01 cri

Fadar shugaban kasar Amurka ta "White House", ta bayyana shirinta na hawa teburin shawara da kasar Koriya ta Arewa, musamman a yunkurin da ake yi yanzu haka na raba zirin Koriyan da makaman nukiliya.

A cewar kakakin fadar gwamnatin kasar ta Amurka Josh Earnest, daukar wannan mataki ya zama wajibi, a dai dai lokaci da Koriya ta Arewan ke bayyana aniyar karbar tayin shawarwarin, bisa wasu sharudda da ta gindaya. Earnest ya kara da cewa, Amurka ta shirya aiwatar da kudirorin da bangarori 6 suka cimma a shekarar 2005, tare da fatan Koriya ta Arewan za ta sauke nauyin dake kanta, na yarda da shirin kawo karshen makaman nukiliya a yankin nata.

A ranar Alhamis din da ta gabata ne dai, kasar Koriya ta Arewan ta yi kira da Amurka, da kuma makwafciyarta Koriya ta Kudu, da su dakatar da abin da ta kira tsokana da suke mata, su kuma janye makaman da suka girke a kewayen yankun Koriya ta Kudu, tare da dakatar da girke sabbi, a matsayin sharadinta na hawa teburin shawara.

A baya bayan nan dai, Amurka da koriya ta Kudu sun sha gudanar da atisayen makaman yaki a yankin, lamarin da ya sanya Koriya ta Arewan yin barazanar kaiwa bangarorin biyu hare-hare da makamai masu cin dogon zango.(Saminu)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China