Kasar demokradiya ta al'ummar Koriya ta Arewa DPRK ta sha alwashin mai da martani da ba tausayi a ciki, muddin makwabciyarta Koriya ta Kudu da kuma Amurka suka yi gigin shiga yankinta a lokacin wani atisayen sojin ruwa da suke yi a kan iyaka da babban tekun Yellow Sea.
Babbar rundunar tsaro ta kudu maso yammacin na bangaren sojin kasar ta DPRK ta ce, dukkan sassan rundunar da kananan sassa za su fara shirin daukar mataki, don haka suna sauraran umurni daga babbar rundunar.
Rundanar ta yi gargadin cewa, muddin kasar Koriya ta Kudu ko Amurka suka kuskura suka yi gangancin harba wani rokansu da suka girke a shiyyar kudu maso yammacin kasar ya shigo kasarta, to lalle wannan shiyyar gaba daya za ta koma tsibirai biyar masu barin wuta wato tekun harshen wuta zalla, wannan kam babu ko tantama a ciki.
Koriya ta Kudu da Amurka sun kaddamar da wani atisayen sojin ruwa na hadin gwiwwa na kwanaki biyar tun daga jiya Litinin a kan tekun Yellow Sea, inda suke amfani da babban jirgin ruwan harbo makamashin nukiliya na Los-Angeles.(Fatimah)