Kasar Koriya ta Kudu ta bayyana shirinta, na kakkabo dukkanin wani makami mai linzami da makwafciyarta Koriya ta Arewa ke barazanar za ta harba mata.
Kakakin ma'aikatar tsaron kasar Kim Min-Seok ne ya bayyana hakan, yayin da yake bayyanawa manema labaru matsayar ma'aikatar ta tsaro. Mr. Seok ya rawaito kalaman ministan tsaron kasarsa, wanda ke cewa, Koriya ta Kudu na da na'urorin kandagarki, wadanda za su iya cafke dukkanin makaman da makwafciyar kasarsu ke kurarin za ta harba.
Kasar Koriya ta Kudu dai a yanzu haka, na amfani ne da na'urorin kandagarki kirar PAC-2, wadanda ke iya harbo makamai masu linzami, da jiragen sama daga nisan kilomita 30.(Saminu)