in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Korea ta arewa ta ce, tana da ma'auni kan aikin samar da makamashin nukiliya
2012-09-06 12:25:08 cri

Jiya ranar 5 ga wannan wata, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Korea ta arewa ya bayyana cewa, bai kamata ba hukumar kula da makamshin nukiliya ta kasa da kasa wato IAEA da kasar Amurka su yi amfani da tsohon ma'auni yayin da suke bukatar ta wato dole ne Korea ta arewa ta samar da makamashin nukiliya domin shimfida zaman lafiya, kasar Korea ta arewa tana da ma'aunin kanta, bai kamata ba hukumar kula da makamashin nukiliya ta kasa da kasa ta tsoma baki a ciki.

Kakakin ya kara da cewa, kwanan baya, hukumar IAEA ta bayar da wani rahoto inda ta nuna damuwa kan gine-ginen "light-water" da sarrafa sinadarin uranium da ake gudanarwa a kasar Korea ta arewa, kakakin ma'aiktar harkokin wajen kasar Amurka shi ma ya bukaci Korea ta arewa da ta daina yin aikin samar da makamashin nukiliya tare kuma da karbar binciken da hukumar IAEA za ta yi mata. Hakan ya sheda mana cewa, hukumar IAEA ba ta gane sosai kan lamarin ba. Har yanzu, hukumar IAEA ba ta taba nuna damuwa kan shirin samar da makamashin nukiliya na sauran kasashe wadanda ke mallakar makaman nukiliya, amma ta nuna damuwa kan shirin makamashin nukiliya na kasar Korea ta arewa kawai, wannan aiki ne rashin adalci.

A wannan rana, kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Korea ta arewa ya nuna matsayi a madadin gwamnatinsa kan shawarwarin share fage tsakanin jami'an gwamnatocin kasashen Korea ta arewa da Japan da aka yi daga ranar 29 zuwa ta 31 ga watan Agustan shekarar bana a birnin Beijing na kasar Sin, inda ya ce, a yayin shawarwarin da aka yi, bangarorin biyu sun bayyana matsayin gwamnatocin kasashensu kan shawarwarin tsakanin gwamnatocin kasashen biyu da za a gudana a hukunce kan batun game da mayar da gawawwakin sojojin kasar Japan da suka mutu a yayin yakin duniya na biyu tare kuma da tattauna sauran hakikanan abubuwan da suka shafi shawarwarin da za a yi kamarsu manyan batutuwan da za'a tattauna, matsayi, wuri, lokaci da sauransu, ban da wannan kuma, sun amince da cewa, za su cigaba da yin musanyar ra'ayoyi tsakaninsu ta hanyar diplomasiya nan gaba.(Jamila)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China