in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta bukaci Koriya ta Arewa da ta daina yin tsokana
2013-04-11 10:12:56 cri

A ranar Laraba, gwamnatin kasar Amurka ta bukaci kasar Koriya ta Arewa DPRK da ta daina yin tsokana sakamakon rahotanni da ake samu na yiwuwar harba makamai daga kasar ta nahiyar Asiya.

Mai magana da yawun gwamnatin kasar Amurka Patrick Ventrell ya ce, Washington na sa ido sosai da kuma aiki da abokanta kan lamarin.

Yayin jawabi ga manema labarai da aka saba yi, ya ce, kamar yadda aka sha nanatawa, idan kasar Koriya ta Arewa ta harba makamai masu linzami, ke nan ta saba nauyi dake wuyanta bisa kudurorin kwamitin sulhu na MDD da dama.

Ya ci gaba da cewa, aikata hakan babu abin da zai haifar illa kara mayar da kasar Koriya ta Arewa saniyar ware da kuma kara gurguntar da ci gaban tattalin arzikinta, don haka ake kira ga kasar da ta kauracema dukkan wani mataki na tsokana.

A kuma ranar Laraba, ministan harkokin wajen kasar Koriya ta Kudu Yun Byung-Se ya bayyana cewa, rahotanni na leken asiri na nuna cewa, akwai alamu, kasar DPRK za ta harba makami mai linzami na gajeren zango a kowane lokaci daga yanzu.

Hankula sun tashi a yankin Koriya tun lokaci da DPRK ta yi gwaji na uku na makaman nukiliya ranar 12 ga watan Fabrairun da ya gabata, don nuna kin amincewarta dangane da atisayen soji na hadin gwiwa tsakanin dakarun Amurka da na Koriya ta Kudu.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China