Ministan dunkulewar Koriya ta Kudu ya gabatar da shawarar yin shawarwari a ranar yau Alhamis tare da Koriya ta Arewa RPDC kan masana'antar Kaesong.
'Muna gabatar wa Koriya ta Arewa wata damar yin shawarwari ta fuskar aiki da kawo agajin jin kai ga ma'aikatan Koriya ta Kudu dake aiki a cikin wannan yanki na masana'antu. Kasar Koriya ta Arewa na da lokaci har zuwa 26 ga watan Afrilu domin amsa wannan tayi.' in ji wata sanarwar hukumomin kasar Koriya ta Kudu a ranar Alhamis.
Za mu daukar muhimman matakai idan RPDC ta yi watsi da wannan tayi, in ji ministan. Koriya ta Kudu ta dauki niyya tun ranar Laraba na kara wa'adin tallafin kudi ga kamfanonin Koriya ta Kudu dake da masana'antu a wannan sansanin masana'antun Kaesong, a yayin da aka dakatar da ayyukansu tun ranar 9 ga watan Afrilu, lokacin da Koriya ta Arewa ta hana shiga wannan sansani ga ma'aikatan kasar dubu 53. (Maman Ada)