A cikin wata sanarwar da aka fitar a ranar Asabar, kwamitin 'yan majalisun kungiyar tattalin arziki da kudi ta yammacin Afrika wato UEMOA ya nuna damuwarsa sosai game da rikicin kasar Mali musammun ma kan dukar da aka yi wa shugaban wucin gadi Mista Dioncounda Traore a yayin wata zanga zanga ta baya baya a Bamako.
Kwamitin CIP da ya gudanar da taronsa karo na goma da sha daya daga ranar 20 zuwa 26 ga watan Mayu a birnin Abidjan na kasar Cote d'Ivoire bisa taken "matsayin majalisar dokoki a wajen tsarin dunkulewa" yayi Allah wadai da tashe tashen hankali na baya baya a kasar Mali, inda Mista Traore da kungiyar ECOWAS ta zaba domin tafiyar da ragamar mulkin wucin gadi a kasar a tsawon watanni 12 ya sha dukar tsiya daga wajen magoya bayan sojojin da suka yi juyin mulki wanda a yanzu haka yake kasar Faransa tun ranar Alhamis domin samun jinya.
Haka kuma kwamitin 'yan majalisun UEMOA ya soki lamarin sabuwar kasar Mali da kuma amfani da karfin tuwo wajen neman ikon kasar in ji sanarwar da shugaba Dama Dramani ya sanyawa hannu.
Daga karshe CIP ya sake nanata fatansa kan girmama fadin kasar Mali da kuma hadin kan kasar tare da jaddada goyon bayansa ga kungiyar ECOWAS kan dukkan matakan da take dauka na neman daidaituwa da girmama tsarin mulkin kasar. (Maman Ada)