Haduwar ta ministoci an bude ta a ranar Lahadi a birnin Banjul a karkashin jagorancin shugaban kasar Gambiya malam Yahya Jammeh tare da halartar manyan jami'an kungiyar ECOWAS da kuma wakilan jam'iyyun siyasa da sojojin da suka yi juyin mulki na kasar Guinea-Bissau.
Tawagar kungiyar ECOWAS da ta hada da kasashen Gambiya, Nijar, Senegal, Togo, Benin da Guinea na da nauyin sanya ido ga aiwatar da matakin da shugabannin kungiyar ECOWAS suka dauka na tura rundunonin sojoji a kasashen Guinea-Bissau da Mali.
Ko da yake sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Guinea-Bissau sun amince da wannan mataki na kungiyar ECOWAS amma sojojin da suka yi juyin mulki a kasar Mali sun yi watsi da shi.
Shugabannin kungiyar ECOWAS sun dauki niyyar sake wata haduwa a ranar uku ga watan Mayu a Banjul domin tattaunawa kan rikicin kasashen na Guinea-Bissau da Mali. (Maman Ada)