in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin ta mika wani babban filin wasa ga kasar Guinea
2012-01-20 16:04:34 cri
Ma'aikatar kasuwanci ta kasar Sin ta ba da labari a shafin internet dinta cewa, kwanakin baya a Conakry, babban birnin kasar Guinea, an yi bikin mika wani babban filin wasan da zai iya kunsar mutane dubu 50, wanda gwamnatin kasar Sin ta sanya aka gina wa gwamnatin kasar Guinea a matsayin wani tallafi ga kasar. Firaministan kasar Guinea, ministan kasar mai kula da hadin kai tsakanin kasa da kasa, ministan wasanni, da dai sauran manyan kusoshin kasar, da Mista Zhao Li, jakadan kasar Sin dake Guinea, gami da jama'ar kasar fiye da dubu 10, sun halarci bikin mika filin wasan.

An ce, filin wasan ya kasance wani tallafi mafi girma a fannin tattalin arziki da kasar Sin take baiwa kasashen yammacin Afirka. Don gina filin wasan an kebe fili da fadinsa ya kai kimanin mita dubu 240, kana fadin ginin kadai ya kai fiye da mita dubu 34, inda aka ajiye kujeru fiye da dubu 50. Filin wasan ya zama irinsa mafi girma da kasar Sin ta gina a kasashen yammacin Afirka. An fara aikin gina filin wasan ne a ranar 18 ga watan Satumba na shekarar 2007, sa'an nan an kammala aikin a ranar 29 ga watan Nuwamba na shekarar 2011. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China