in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Guinea ya yi shelar gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a ranar 30 ga watan Yuni
2013-04-14 17:09:16 cri
A daren ranar Asabar 13 ga wata, shugaban kasar Guinea, Alpha Condé ya bayyana ta gidan talibijin na kasar cewa, za a gudanar da zaben majalisar dokokin kasar a ranar 30 ga watan Yuni mai zuwa, zaben da aka jinkirta gudanar da shi tsawon sama da shekaru 2, shugaban ya kuma yi kira ga jama'ar kasar da su kada kuri'a cikin yakini.

Bisa sanarwar za a gudanar da zaben a ranar 30 ga watan Yunin ne a dukkanin fadin kasar, tun daga karfe 7 na safe, har zuwa karfe 6 na yamma. Alpha Condé ya bukaci kwamitin zabe mai zaman kansa, da ma'aikatar kula da harkoki cikin gida, da ragowar masu ruwa da tsaki, dasu share fagen gudanar zaben, a kokarin samun nasarar zaben a kan lokaci.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, wannan ne karo na farko da shugaban kasar ya ba da sanarwar tabbatar da lokacin gudanar da zaben majalisar dokokin kasar. Kafin dai hakan kwamitin zaben kasar mai zaman kansa ya sha tabbatar da lokacin zaben, sai dai an yi ta jinkirta zaben a sakamakon rashin amincewar da jam'iyyun adawa suka nuna.

Bayan babban zaben kasar Guinea a shekarar 2010, jam'iyyar dake rike da madafan ikon kasar, da jam'iyyun adawa, sun kasa cimma matsaya daya, a sabili da haka, aka yi ta dage gudanar da wannan zabe.

Wannan matsala dai a baya ta sha kaiwa ga zubar da jini, inda mutane sama da 10 suka rasu a sakamakon haka. A kwanan baya kuma, jam'iyyar kasar mai mulki ta yi shelar amincewa da wasu bukatun jam'iyyun adawa, inda sabili da haka, dangantaka tsakaninsu ta sami kyautatuwa, aka kuma fara farfado da shawarwari tsakaninsu a siyasance. (fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China