A yayin wannan ziyara dake cikin tsarin karfafa dankon zumunci tsakanin kasashen biyu, za'a shirya wani gagarumin biki a zauren " Palais du peuple " dake birnin Conakry, inda shugabannin biyu za su gabatar da jawabi ga al'ummar kasar Guinea da kuma 'yan kasar Nijar dake zaune a kasar ta Guinea.
Hakazalika za'a gudanar da shawarwari tsakanin tawagogin kasashen biyu kan muhimman batutuwan da suka fi janyo hankalinsu kamar batun karfafa hulda da abokantaka da za su taimakawa moriyar kasashen biyu. (Maman Ada)