in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za ta ci gaba da ba da gudummawarta don warware batun Mali
2013-05-23 21:03:46 cri

Kakakin ma'aikatar harkokin waje ta kasar Sin Hong Lei ya bayyana yau Alhamis 23 ga wata, cewar kasar Sin za ta ci gaba da ba da gudummawarta don warware batun kasar Mali.

Wani jami'in MDD ya yi furuci a ranar 22 ga wata cewa, kasar Sin za ta tura sojoji masu kiyaye zaman lafiya fiye da 500 don shiga rundunar MDD masu kiyaye zaman lafiya a kasar Mali.

Game da wannan, Hong Lei ya ce, ko da yaushe kasar Sin na zura ido kan halin da kasar Mali ke ciki, kuma ta nuna goyon baya ga kokarin da gwamnatin kasar Mali da MDD da sauran kungiyoyin duniya da na shiyya shiyya ke yi domin kiyaye ikon mallakar Mali da cikakken yankunan kasar kana da zaman lafiya a wannan yanki. Haka kuma Sin ta mara baya da a aiwatar da kudurori masu lamba 2085 da 2100 da kwamtin sulhu na MDD ya gabatar.

Hong ya kara da cewa, ana fatan kasashen duniya za su ci gaba da tallafa wa Mali wajen sulhunta al'ummarta, zaman karko da zaman lafiya cikin hanzari. (Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China