in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Wakilin musamman na shugaban kasar Korea ta arewa ya mikawa shugaban kasar Sin wasikar shugaban kasar
2013-05-24 20:32:43 cri

Yau Juma'a 24 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin Mr Xi Jinping ya gana da Choe Ryong-hae, wakilin musamman na shugaban kasar Korea ta arewa kuma wakilin dindindin na ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na Jam'iyyar WP ta kasar Korea ta arewa. Yayin ganawar, Choe Ryong-hae ya mikawa Xi Jinping wata wasika da shugaba Kim Jong-un na kasar Korea ta arewa ya rubuta.

Mr Xi ya nuna cewa, dankon zumunci dake tsakanin Sin da Korea ta arewa na dacewa da moriyar kasashen biyu da jama'arsu. Jam'iyyar JKS da kuma gwamantin kasar Sin na fatan kara hadin kai da Korea ta arewa domin ingiza dangantakar dake tsakaninsu yadda ya kamata cikin dogon lokaci.

Mr Xi ya kara da cewa, kawar da makaman nukiliya a zirin Korea da tabbatar da zaman lafiya mai dorewa buri ne na dukan fadin duniya kuma ya kasance hanyar da dole a zaba. Sin na nacewa ga matsayin da take dauka na cewa, ya kamata bangarori daban-daban da abin ya shafa su kawar da makaman nukiliya a zirin ta hanyar yin shawarwari duk da sauyin halin da ake ciki. (Amina)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China