Ban da wannan kuma, shugaba Xi ya yi nuni da cewa, da farko, kamata ya yi a ba da goyon baya ga bin manufar kafa kasar Palesdinu cikin 'yancin kai, da kasancewar kasashen biyu na Falesdinu da Isra'ila cikin lumana. Na 2, ya zama wajibi a mayar da shawarwari a matsayin hanyar da za a bi wajen cimma burin samar da zaman lafiya tsakanin Falesdinu da Isra'ila. Na 3 kuma, ya zama dole a nace kan ka'idar "mai da yankunan kasa domin samun zaman lafiya", a karshe dai, kamata ya yi kasashen duniya su ba da tabbaci ga yunkurin shimfida zaman lafiya a wannan shiyya.
A nasa bangare kuma, Abbas ya jaddada cewa, hanyar siyasa ita ce hanya mafi kyau wajen warware batun Falesdinu. Hukumar Falesdinu tana dukufa ka'in da na'in don cimma burin samun sulhu cikin zaman lafiya. Haka kuma, Falesdinu tana fatan kasar Sin za ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa.
Bayan shawarwarin, shugabannin kasashen biyu sun halarci bikin rattaba hannu da daddale yarjejeniyoyin hadin gwiwa kan musayar fasahohin tattalin arziki da al'adu da ilmi tsakaninsu.(Bako)