in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Xi Jinping ya jadadda cewa a gaggauta ayyukan gina tsibirin yawon shakatawa na kasa da kasa a lardin Hainan
2013-04-11 11:36:31 cri

Tun daga ranar 8 zuwa 10 ga watan Afrilu, yayin da babban sakataren kwamitin tsakiyar jam'iyyar kwaminis ta Sin, kuma shugaban kasar, Xi Jinping yake ziyarar aiki a lardin Hainan na kasar Sin, ya jadadda cewa, Hainan ya kasance yankin musamman mafi girma a kasar baki daya a wajen samun bunkasuwar tattalin arziki.

Hakan ya sa yankin na da kyakyawar dama wajen ci gaba da neman bunkasuwarsa cikin dogon lokaci, musamman ma a fuskar gina tsibirin yawon shakatawa na kasa da kasa, wanda zai iya kafa wata hanyar ci gaba da ta bambanta da dukkan hanyoyin da aka taba bi wajen neman bunkasuwa.

Shugaba Xi ya kuma jadadda cewa, manufar gaggauta ayyukan gina tsibirin yawon shakatawa a lardin Hainan wata muhimmiyar shawara ce da gwamantin kasar Sin ta tsayar, kuma ta dace da halin lardin Hainan wajen neman bunkasuwa sosai.

Mr. Xi Jinping yana mai da hankali sosai kan harkokin kiyaye al'adun halittu a yankin Hainan, inda ya bayyana cewa, yanayin halittu wani kyakkyawan alheri gare mu wajen zaman rayuwa cikin muhalli mai kyau, wanda zai kuma iya fitar da moriyar tattalin arziki ga jama'ar kasa.

Ya ci gaba da cewa, kamata ya yi mu kiyaye muhallinmu a fannoni da suka hada da tsaunuka da koguna, sararin sama da teku, da dai sauransu don gina tsibirin yawon shakatawa na kasa da kasa.

Bugu da kari, ya nuna fatan cewa, gwamnatin lardin Hainan za ta iya daidaita dangantakar neman bunkasuwa da kiyayen muhallin yankin, don neman ci gaba na tsawon lokaci, wanda zai wadatar da zuri'armu 'yan baya.

Haka zalika, shugaba Xi ya bayyana cewa, kamata ya yi gwamnatin lardin Hainan ta yi amfani da manufofin bunkasa sha'anin yawon shakatawa da gwamnatin kasa ta bayar yadda ya kamata, don raya harkokin masana'antun ba da hidima na yankin, musamman ma a fuskar sha'anin yawon shakatawa. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China