in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban kasar Sin ya gana da ministan harkokin wajen Faransa
2013-04-12 20:15:35 cri
Ranar 12 ga wata, shugaba Xi Jinping na kasar Sin ya gana da Laurent Fabius, ministan harkokin wajen kasar Faransa a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar, shugaba Xi ya ce, ya yi imanin cewa, dangantakar da ke tsakanin Sin da Faransa ba kawai za ta kawo wa kasashen 2 da jama'arsu duka alheri ba, hatta ma za ta taimaka wajen kafa sabon tsarin hadin gwiwa domin samun moriyar juna a tsakanin kasashe masu sukuni da kasashe masu tasowa, haka kuma za ta taimaka wajen kara azama kan raya duniya a matakai daban daban da kuma sanya dimokuradiyya kan dangantakar da ke tsakanin kasa da kasa.

Shugaba Xi ya kara da cewa, kasar Sin na daukar ziyarar aiki da shugaba Francois Hollande na Faransa zai kawo mata ba da dadewa ba da muhimmanci sosai, don haka yana sa ran yin musayar ra'ayoyi tare da shugaban na Faransa Hollande dangane da dangantakar da ke tsakanin kasashensu da al'amuran da ke jawo hankalinsu, a kokarin samun ra'ayi daya da habaka hadin gwiwa.

Shi kuma a nasa bangaren, mista Fabius ya ce, Faransa da Sin na tsayawa kan bin manufar 'yancin kai ba tare da tsangwama ba a harkokin waje, suna kuma himmantuwa wajen tabbatar da samun zaman lafiya da kwanciyar hankali da bunkasuwa a duk duniya baki daya. Shugaba Francois Hollande zai kasance shugaba na farko da ya fito daga manyan kasashen yammacin duniya da zai kawo ziyara tun bayan da shugaban kasar Sin ya haye kujerar mulkin kasa, don haka ministan ya yi imanin cewa, ziyarar shugaba Francois Hollande za ta kara sabon karfi wajen kyautata hulda a tsakanin Faransa da Sin.(Tasallah)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China