Yayin da yake ganawa da Mr Kissinger, shugaba Xi Jinping ya bayyana cewa, ana bukatar kasashen biyu su yi kokari tare wajen inganta sabuwar dangantakarsu. Kana kasashen biyu su kara yin hadin gwiwa da yin mu'amala kan batutuwan kasa da kasa da kuma na yankuna, ta yadda dangantakarsu za ta bunkasa yadda ya kamata.
Mr Kissinger ya ce, kamata ya yi Amurka da Sin su kara yin mu'amala da hadin gwiwa kan manyan batutuwan da suke shafar zaman lafiya, ta yadda za a taimaka wajen kiyaye dawamammen bunkasuwar dangantakarsu tare da tabbatar da zaman lafiya da samun ci gaba a fadin duniya gaba daya.
Yayin da yake ganawa da Mr Paulson, shugaba Xi Jinping yana sa kaimi kan cibiyar Paulson da ta ci gaba da taka muhimmiyar rawa wajen inganta dangantakar kasashen biyu.
A nasa bangare Mr Paulson ya bayyana cewa, a halin yanzu, kasashen biyu suna fuskantar dama da kalubale a fannonin farfado da tattalin arziki, makamashi, kiyaye muhalli, sauye-sauyen yanayi da dai sauransu, don haka ya kamata su kara yin hadin gwiwa a tsakaninsu. (Zainab)