in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin da Afirka za su hada kansu don cimma burin samun farfadowa tare, in ji shugaban kasar Sin
2013-05-13 19:57:27 cri

Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya jaddada a yau litinin 13 ga wata a nan birnin Beijing, cewa kasar Sin za ta ci gaba da goyon bayan kasashen Afirka da kokarin da suke yi don samun zaman lafiya da bunkasuwa kamar yadda ta kan yi kullum, a kokarin hadin kansu don cimma burin samun farfadowa tare.

Shugaba Xi wanda ya fadi haka a ganawar da yayi da takwaransa na kasar Mozambique Armando Guebuza da ke ziyarar aiki a nan kasar,ya lura cewa nan ba da jimawa ba, kasashen Afirka da jama'arsu za su yi bikin murnar cika shekaru 50 da kafuwar kungiyar tarayyar Afirka, ta hakan Afirka za ta bude wani sabon shafi wajen sha'anin zaman lafiya da bunkasuwa.

Ya kuma jaddada cewa idan har kasashen Afirka na son cimma burin samun farfadowa, to dole ne su samu kwanciyar hankali, da hadin kansu, da kuma samun wata hanyar ci gaba da ke dacewa da halin da suke ciki.

A nasa bangaren, shugaba Guebuza ya tabbatar da cewa kasar Sin na taka muhimmiyar rawa wajen samun zaman lafiya da karko da kuma ci gaba a Afirka don haka a ganinsa akwai makoma mai haske wajen hadin gwiwar bangarorin biyu, shi ya sa kasar Mozambique ke son mai da hankali wajen bunkasar huldar da ke tsakanin Afirka da Sin.(Kande Gao)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China