in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban Zimbabwe ya sanya hannu kan kundin tsarin mulkin kasar
2013-05-22 20:14:33 cri
A yau ne Laraba 22 ga wata ne shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya sanya hannu kan kundin tsarin mulkin kasar da aka yi wa gyaran fuska, matakin da ya bada damar maye gurbin kundin tsarin mulkin da kasar ke amfani da shi a halin yanzu a jajiberin bikin samun 'yancin kan kasar daga Birtaniya shekaru 33 da suka gabata.

Sanya hannu kan kundin tsarin mulkin kasar da shugaban kasar ya yi, ya kawo karshen shirin da aka fara kusan shekaru 4 da suka gabata, ganin cewa, matakai kadan ne kawai suka rage kafin wasu sassan kundin tsarin mulkin kasar su fara aiki ka'in da na'in, yayin da za a fara gudanar da 'yan gyare-gyare a wasu sassan.

A jawabinsa yayin bikin sanya hannun da aka yi a majalisar dokokin kasar, ministan kula da dokoki da harkokin majalisu na kasar Eric Matinenga ya ce, "wannan abin tarihi ne, ganin yadda kundin tsarin mulkin zai mana jagora nan gaba." (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China