An labarta cewa, bankin raya kasashen BRICS zai samar da asusun hadin gwiwa domin taimakawa wajen gudanar da ayyukan more rayuwar jama'a da inganta karfin muhimman hukumomin da abin ya shafa. Bankin zai kara goyon baya da kara azama kan yin hadin gwiwa a tsakanin kasashen BRICS da sauran sabbin rukunonin tattalin arziki ta fuskar cinikayya. Bankin zai kafa wani asusu mai yawan dalar Amurka biliyan 50, wanda aka sa ran cewa, zai mara bayan wasu ayyukan more rayuwar al'umma tsakanin kasa da kasa a nahiyar Afirka.
Kwanan baya, Sandile Zungu, sakataren kwamitin harkokin kasuwanci na Afirka ta Kudu ya bayyana wa manema labaru cewa, kasashen BRICS suna gudanar da manyan ayyukan more rayuwar jama'a, amma ka'idoji da sharuddan da ake bi ta fuskar ba da rancen kudi suna kawo cikas kan saurin bunkasuwar tattalin arziki, don haka ya zama wajibi a kafa bankin raya kasashen BRICS.(Tasallah)