in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Babban jami'in AU ya ce, hulda tsakanin Sin da Afirka na samun bunkasa da dorewa
2013-03-26 10:30:21 cri

Wani babban jami'in hukumar gudanar da kungiyar hada kan kasashen Afirka AU ya ce, kungiyar na ci gaba da aiki tare da kasar Sin don a samu bunkasa da kuma dorewar dangantaka tsakaninsu.

Mataimakin shugaban hukumar kungiyar AU, Erastus Mwencha ya bayyana wa kamfanin dillancin labaran kasar Sin, Xinhua yayin wata hira kafin a fara taron kungiyar BRICS jiko na biyar daga yau 26 zuwa 27 ga watan Maris cewa, Afirka da kasar Sin sun amince da kara bunkasuwa da kuma inganta huldar tsakaninsu wadda suka kulla sama da shekaru 50 da suka gabata.

Ya ci gaba da cewa, kasar Sin ta taka muhimmiyar rawa a fuskar ba da goyon baya ga nahiyar Afirka a yunkurinta na samun 'yancin kai, inda ya ba da misali da layin dogo da ya hade kasar Tanzaniya da Zambiya wanda kasar Sin ta taimaka wajen ginawa tsakanin shekarun 1970 zuwa 1975.

Ya ci gaba da cewa, a yanzu haka Afirka da kasar Sin na cin amfanin hadin kan dangantakarsu karkashin dandalin hadin kan Sin da Afirka (FOCAC).

Ya ce, kasar Sin ita ce ke kan gaba a fuskar huldar kasuwanci da Afirka, inda harkar cinikayya tsakaninsu ya haura daga dalar Amurka biliyan 10 a shekara ta 2000 zuwa dala biliyan 160 a halin yanzu.

Da kuma ya waiwayo kan taron BRICS da za'a yi a Durban ta kasar Afirka ta Kudu, Mwencha ya ce, an gayyaci hukumar kungiyar AU da sauran kungiyoyin bunkasa tattalin arziki na yankuna (RECs) domin su samu duba batutuwan da suka shafe su kamar tabbatar da dorewar tattalin arzikin duniya da kuma bullo da dabarun zuba jari.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China