A cewar Qin Gang, yayin ganawarsa da sakataren harkokin wajen kasar Amurka, John Kerry, wanda ya kawo ziyarar aiki kasar ta Sin a kwanakin baya, bangarorin 2 sun tattauna batutuwan da suka shafi musayar ra'ayi da manyan jami'an kasashen 2 za su yi ta fuskar harkokin al'adu, da shawarwari a fannin manyan tsare-tsare da tattalin arziki, inda suka cimma ra'ayi daya. Ya kuma ce a bangaren kasar Sin, an sanya mataimakiyar firaministan kasar, Madam Liu Yandong, ta ci gaba da zama a matsayin shugaba mai kula da musayar ra'ayi kan harkokin al'adu, kana an sanya Wang Yang, wanda shi ma ke matsayin mataimakin firaministan kasar, da mamban majalisar gudanarwar kasar Yang Jiechi, domin kula da shawarwari a fannin tattalin arziki da manyan tsare-tsaren kasashen 2.(Bello Wang)