Wannan ne karo na farko da John Kerry ya kawo wa kasar Sin ziyara bayan da ya hau kan mukaminsa. Wannan ne kuma wani muhimmin jigo na daban da ya kawo wa kasar Sin ziyara domin ganawa da muhimman jigunan kasar Sin bayan da Jacob Lew, wakilin musamman na shugaba, kuma ministan kudi na gwamnatin kasar Amurka ya kawo ziyara kasar Sin a watan Maris bayan da aka rantsar da sabbin gwamnatocin kasashen Sin da Amurka.
Bisa labarin da ma'aikatar harkokin wajen kasar Sin ta bayar, an ce, a yayin ziyararsa a nan kasar Sin, shugabannin kasar Sin za su gana da shi, inda za su yi musayar ra'ayoyi kan huldar dake tsakanin kasashen Sin da Amurka da sauran batutuwan da suke jawo hankulansu tare.
Wannan ne kuma zango na biyu cikin ziyararsa ta kasashen gabashin Asiya guda uku. Kafin ya zo kasar Sin, ya riga ya kai ziyara a kasar Koriya ta kudu, sannan zai kai ziyara ga kasar Japan gobe ranar 14 ga wata. (Sanusi Chen)