in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugabannin Sin sun gana da shugaban taron hafsoshin sojojin kasar Amurka
2013-04-23 20:28:16 cri
A ranar 23 ga wata a nan birnin Beijing, shugaban kasar Sin kuma shugaban kwamitin aikin soja na tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Xi Jinping ya gana da shugaban taron hafsoshin sojojin kasar Amurka Martin E. Dempsey tare da tawagarsa.

A yayin ganawar, Xi Jinping ya jaddada cewa, kiyaye bunkasuwar dangantakar sojojin kasashen Sin da Amurka zai taimaka wajen kara fahimtar juna a tsakaninsu, da kuma magance abkuwar rikice-rikice. Shugaba Xi Jinping ya ce, fiye da shekara daya da yanzu, sojojin kasashen biyu sun samu ci gaba a fannonin ganawar shugabanninsu, yin shawarwari, yin atisayen soja na hadin gwiwa da dai sauransu. Don haka kasar Sin tana son yin kokari tare da kasar Amurka wajen kara fahimtar juna a fannin aikin soja, da kuma fadada hadin gwiwa don inganta sabuwar dangantakar aikin soja a tsakaninsu

A nashi bangaren Martin Dempsey ya bayyana cewa, ziyararsa a wannan karo ta kasance muhimmin kashi na ayyukan da shugabannin kasashen biyu suka tsara a wannan fanni. Domin sun yi shawarwari cikin 'yanci, da samun nasarori a ciki. Haka kuma Dempsey ya ce, kasar Amurka tana son yin kokari tare da kasar Sin wajen kara fahimtar juna, kawar da matsaloli, da kuma inganta dangantakar sojojin kasashen biyu bisa manufofin da shugabannin kasashen biyu suka tsara.

Ban da wannan kuma, mataimakin shugaban kwamitin aikin soja na tsakiya na jam'iyyar kwaminis ta kasar Sin Fan Changlong, ministan tsaron kasar Chang Wanquan da kuma memban majalisar gudanarwar kasar Yang Jiechi sun gana da Dempsey. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China