A cikin jawabinsa kafin kammala ziyarar, Netanyahu ya bayyana cewa, an samu cikakkiyar nasara game da ziyarar, inda kasashen biyu suka amince da kafa wata kungiyar musamman dake kunshe da jami'an bangarorin biyu, don karfafa hadin gwiwa a fannonin kimiyya da fasaha, tattalin arziki da cinikayya da dai sauransu. Wannan babban ci gaba ne da suka samu, wanda kuma ke da ma'ana sosai ga Isra'ila.
Yayin da yake kasar Sin ya taba bayyana cewa, kasashen Sin da Isra'ila suna cudan-bayan -juna don tabbatar da zaman lafiyar kasuwanni tare.
Kafin Netanyahu ya iso nan birnin Beijing kuma, shugaban Falestinu Mohmoud Abbas ya kammala ziyara a kasar Sin ba da dadewa ba. Hakan ya sa aka yi tsammanin cewa, ko bangarorin biyu za su yi ganawa a birnin Beijing.
A nasu bangaren kuma, kafofin watsa labaru na kasar Isra'ila su ma sun mai da hankali sosai kan ziyarar da shugabannin biyu suka yi a Sin. A sa'i daya kuma, wasu kafofin watsa labaru sun yi nazarin cewa, kasar Sin na sa himma kan warware matsalar Falestinu ne domin ta kara karfinta na yin tasiri a yankin gabas ta tsakiya. (Bilkisu)