A wannan rana, kwamitin sulhu na MDD ya jefa kuri'u kan shirin kuduri dangane da adawa da ci gaba da gina matsugunan Yahudawa da Isra'ila ke yi. Amma, saboda kasar Amurka ta ki amincewa da kudurin, ba a zartas da shi ba. Ban da kasar Amurka, sauran kasashe 14 da ke kwamitin sulhun dukkansu sun jefa kuri'ar amincewa da kudurin.
Wakilin dindindin na kasar Sin da ke MDD, Li Baodong ya yi bayani bayan taron cewa, kasar Sin na nuna bakin ciki kan rashin zartas da kudurin. Ya kara da cewa, ci gaba da gina matsugunan Yahudawa da kasar Isra'ila ke yi na kawo babban cikas ga nuna amincewa ga juna, da sake maido da shawarwarin zaman lafiya a tsakanin Falestinu da Isra'ila. Ya jaddada cewa, a kullum kasar Sin na tsayawa tsayin daka kan kawar da bambanci tsakanin bangarorin biyu ta hanyar yin shawarwari, kuma bisa tushen kudurin da abin ya shafa na MDD, da manufar "ba da kasa domin samun zaman lafiya", da shawarwarin zaman lafiya na Larabawa, da kuma muhimman tsare-tsare na shirin 'Taswirar shimfida zaman lafiya ' a Gabas ta Tsakiya, domin cimma burin kafa kasar Falestinu, da yin zama tare cikin lumana tsakanin bangarorin biyu a karshe. (Bilkisu)